An kama wani mutum da laifin saduwa da majinyaciya a gadon asibiti

Ana tuhumar wani magidanci da laifin shiga asibi ya sadu da matarsa bayan matar tana kan gado tana jinya.

Mutumin da asalin kasar Zimbabwe ya shiga asibitin masvingo provincial hospital  da misalin karfe 3 na dare ya kuma tilastawa matarsa saduwa dashi.

An ruwaito cewa Mutumin yaje asibitin ya nunawa masu gadi cewa lallai saiyaga matarshi a daren inda sukaita rigima daga baya suka barshi yashiga sai kuma majinyata suka lura cewa wani alamari mai kama da saduwa yana faduwa a bangaren. Majinyata ne suka sanarwa masu gadin wurin abinda ke daruwa inda akazo aka tarar dashi. Mutumin ya sadu da matarshi a wurinda akwai majinyata 10 da suke kwance kusa da matarshi.

Matar ta sanarwa ‘yan uwanta majinyata cewa mijinta ya tilasta mata kuma idan taki amincewa zai iya dukanta akan haka.

Yanzu haka dai an mika mai laifin hannun jamian tsaro don bincike akan dalilin aukuwar lamarin.

Source: https://ift.tt/2MkI1p5

Leave A Reply

Your email address will not be published.