An Kama Wasu Tsofaffin Jamian Yan Sanda Bisa Zargin Yin Garkuwa Da Mutane

Rundunar ‘yan Sandan Najeriya, ta damke wasu tsofaffin ‘yan Sanda, da suke taimakawa wajan satar Shanu, fashi da garkuwa da mutane domin amsan kudin fansa.

Wadanda aka damke sune ASP Yuguda Abba, Sgt. Habila Sarki, Diphen Nimmyel, Sgt. Yasan Danda, Sgt. Abbas Mailalle, Sgt. Bwanason Tanko, Sgt. Donan James CPL. Idris Salisu da CPL. Zakari Kofi.

Kakakin ‘yan Sanda mataimakin kwamishinan ‘yan Sanda Don Awunah, yace an yiwa mutanen hukuncin na cikin gida kamar yadda doka ta tanada.

Ya kara da cewa tumumar da aka yiwa wadannan mutane da jawaban da suka yiwa ‘yan Sanda ya taimakawa jami’an wajan cafke wasu mutane goma sha tara da kuma kwato bindigogi goma sha shida da albarusai da dama.

Leave A Reply

Your email address will not be published.