An Yi Wa Wani Babban Malami Da Iyalinsa Kisan Kare Dangi a Jahar Ogun

 sheikh Yusuf amzat salam

An Yi Wa Wani Babban Malami Da Iyalinsa Kisan Kare Dangi a Jahar Ogun

Wani babban malami mai suna Yusuf Amzat-Salam da shi da iyalinsa sun gamu da ajalinsu a daren ranar Talatar da ta gabata, bayan da wasu da ba a san ko su wane ba suka sassara su gaba daya da adda.

An samu Malamin mai shekaru 35 da matar sa da ‘yayan sa guda hudu a cikin jini da safiyar ranar Talata a lokacin da motar makaranta ta je daukar ‘yayan.

‘Yayan sun kunshi yarinya mai shekaru 11, ‘yan biyu maza masu shekaru 8 da kuma ‘yar autan gidan mai shekaru 2. Tuni an binne su kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

Jama’ar unguwar Atiba da ke karamar hukumar Odogbolu inda malamin ke zaune sun bayyana shi a matsayin mutum mai kamala da son mutane, wanda ba ya fada da kowa.

Kanin marigayin mai suna Ishaaq Amzat-Salam ya shaidawa kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya cewa ya bar batun a wajen ubangiji, wanda shi kadai zai iya yi masu sakayya.

Senator mai wakilatar Gabashin Ogun Gbenga Kaka wanda ya halarci wajen jana’izar ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki da ban al’ajabi.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jahar Ogun, Bimbola Oyeyemi, ya ce su na sane da faruwar lamarin kuma har sun fara bincike a kai.

Leave A Reply

Your email address will not be published.