An Yiwa Wata Mata Yankan Rago A Jihar Kano

Daga Aminu Abdu Baka Noma Sani Mainagge, Kano

Lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar din da ta gabata a wata Unguwa mai suna Sha’iskawa dake karamar hukumar Dambatta, inda aka riski amaryar mai suna Khadija cikin jini a malale tare da wuka a wuyanta. Sannan kuma har zuwa yanzu ba a san ko su wane suka aikata wannan lamari ba.

A yayin da wakilinmu ya ziyarci gidan da abin ya faru, ya zanta da surukar marigayyar sakamakon mijin matar da aka yanka yau kwanansa uku da komawa Abuja bayan kammala hutun Sallah.

Mahaifiyar mijin ta shaida cewar ta je dakin mai rasuwar ne domin ta tashe ta ta yi sahur domin daukar Azumin Sitta Shawwal, amma ta yi ta buga mata kofa shiru, inda tana bude kofar sai ta same ta cikin jini an yi mata yankan rago.

Leave A Reply

Your email address will not be published.