Ana Batawa Ministocina Suna Inji Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Ana zargin Mista Kachikwu da almundahana a shirin gwamnati na musayar danyen mai da tatacce

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya yi kira ga ‘yan kasar da su yi watsi da duk wani batu na bata sunan minsitocinsa da ake yi da sunan cin hanci ba tare da kwakkwarar hujja ba.

Shugaba Buhari ya fadi haka ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkar yada labarai Femi Adesina, ya fitar, in da yake mayar da martani kan wasu rahotanni da kafafen yada labarai ke yadawa a kan karamin ministan man fetur na kasar.

Rahotannin dai na cewa ana bincikar Mista Ibe Kachikwu, kan almundahana a shirin gwamnati na musayar danyen mai da tatacce a lokacin da yake shugaban kamfanin man fetur na kasar NNPC.

Sanarwar ta ce, shugaba Buhari ya yi kira ga mutane da su guji yin kalaman batanci ga mutanen da ke bautawa kasar.

“Bai kamata a dinga munanan kalamai ba na cin mutuncin mutane. Ba za mu yi kasa-a-gwiwa ba wajen ganin mun binciki duk wanda aka samu da almundahana, amma kamata ya yi mutane su jira har sai an samu mutum da laifi dumu-dumu,” in ji shugaba Buhari.

Ya kuma kara jadda aniyar gwamnatinsa ta gaskiya da dattako, yana mai alkawarin cewa za a yi bincike kan duk abin da ya dace cikin adalci.

Baya ga Mista Kachikwu, akwai wasu manyan jami’an gwamnatin da kuma ake alakantawa da hannu a badakalar sayen makamai, lamarin da gwamantin ta musanta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.