Anga Sunan Sarkin Kano A Jikin Wata Laya Da Aka Daurawa Mujiya

An Ga Sunan Sarkin Kano A Jikin Wata Laya Da Aka Daurawa Mujiya

Daga Balarabe Yusuf Gajida

Al’ummar Lokon Kamfa dake unguwar Mandawari a cikin birnin Kano ne suka ga wannan mujiya da laya tana shawagi a cikin dare, bayan da Allah ya sa wannan mujiya ta fado an samu wadanda suka bude layar suka ga abin da ke ciki.

Zuma Times Hausa ta samu ganin wannan rubutu dake cikin layar, wanda aka gano rubutun wata aya ce a cikin Alkur’ani mai girma, aya ta 65 cikin suratul Yasin.

A cikin ayar an bude girman munjayen da yake cikin ayar, inda aka ga an rubuta sunan Sunusi Lamido Sunusi, Sarkin Kano mai ci.

Shin anya kuwa wannan ba wani sharri ko mugunta wani ke kulla masa ba?

Lallai da ake cewa, biri ya so ya yi kama da mutum. Domin in kun tuna a kwanakin baya bayan nan, mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na ll ya fuskanci barazana mai tsanani da har aka fara wani bincike a kansa, sakamakon wasu korafe korafe da aka ce an yi game da yadda yake tafiyar da harkokin sa na mulki.

Allah dai ya kara kare imanin mu da mutuncin mu.

©Zuma Times Hausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.