Anyiwa Matar Data Haifi ‘Yan Biyar Kyautan Katafaren Gida A Abuja

An Yi Wa Matar Da Ta Haifi ‘Yan Biyar Kyautar Katafaren Gida A Abuja

Daga Aliyu Ahmad

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya Winifred Oyo-Ita tare da hadin gwuiwar kamfanin gini na EFAB sun mika takardar katafaren gida mai dakuna uku ga iyayen da suka haifi ‘yan biyar a babban asibitin Abuja.

Misis Oyo-Ita ta gabatar da takardar gidan ne ga mahaifin yaran, Imudia Uduehi a yayin wani taro da aka gudanar jiya a Abuja.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai, Misis Oyo-Ita ta yi alkawarin baiwa iyayen jariran gida.

Gidan dai yana a yankin Dakwa ne kusa da Deidei Abuja.

Kallesu CIKIN HOTUNA.

® Aliyu Ahmad

Leave A Reply

Your email address will not be published.