Atiku ne kadai zai iya kayarda Buhari -Inji wani mai sharhin siyasa

Wani matashi Boladele Adekoyo mai sharhi akan siyasa da kuma lamuran yau da kullum yace tshohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ne kawai PDP zata  iya tsayarwa kuma ya kayarda shugaba Buhari dake kan karagar mulki.

Matashin yace duba da yadda siyasar nigeria take ba irin ta sauran kasashe ba saboda yadda ake amfani da kudi da kuma karfin iko wajen tsayarda dan takara.

A shekarar 2014 lokacinda akayi zaben fidda gwani a APC kowa na ganin yadda Bola Ahmed tinubu yayi iya kokarinsa saida aka mayarda zaben jihar lagos maimakon filin Eagle Square Abuja. Kuma da ace anyi zaben a Abuja lallai kwankwaso ne zai lashe ganin haka yasa Tinubu ya maida zaben lagos yayi amfani da damarsa a jihar har saida ya tabbatar Buhari ne ya lashe zaben.

Yace” babbam dallili da yaza Atiku Abubakar yafi dacewa da a tsayar dashi shine yanada kwarewa a harkar zamantakewa musamman ganin irin yadda yake kokari awajen zayyana abubuwan cigaba da Kum ayyana kyakyawan gobe ga matasan Nigeria.

“Dukda cewa kwankwaso yanada kananan shekaru kuma yanada mabiya da Kum masoya bazai kai Atiku karfi wajen kayarda shugaba da yake kan kujera ba saboda yawanci saaninsa a siyasa ba lallai su goyi bayansa ba.

“Atiku ya zama wani jigo a  siyasa wanda duniya tasan haka kuma na tabbata idan har zai samu goyon bayan gomnonin PDP da kuma masu fada aji a Nigeria to zai iya lashe zabe saboda cancantarsa.

Via: Vanguard newspaper

Source: https://ift.tt/2MjJkDN

Leave A Reply

Your email address will not be published.