Babbar Matsalar Matan Fim Bakin Ciki Da Kishi –In Ji Rahama Sadau

 Rahama Sadau

Babbar Matsalar Matan Fim Bakin Ciki Da Kishi –In Ji Rahama Sadau

Daga Auwal M. Kura

Korarriyar ‘yar wasan shirya finafinan Hausar nan kuma haifaffiyar garin Kaduna wato Rahama Ibrahim Sadau ta bayyana bakin ciki  da kuma hasada a matsayin babbar matsalar da ta da baibaiye matan dake cikin masana’antar fim ta Kannywood.

Ta kuma yi zargin cewa da yawa daga cikin matan suna da girman kai, sannan suna amfani da sana’ar wajen biya wa kansu bukatun su kuma hakan ba karamin zubar wa da ‘yan fim da daraja yake yi ba -in ji Rahama Sadau.

Babu shakka wannan babban kalubale ne dake bukatar sabbin shugabannin kungiyar masu shirya finafinai ta MOPPAN da aka zaba a karshen makon da ya gabata, su fara karyawa da shi, domin kara inganta darajar harkar fim din Hausa.

© www.KannyMp3.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.