Baje Kolin Rahama Sadau A Social Media Wani Irin Alfanu Ta samu Gareku Masoya
RAHAMA SADAU
Ana yi wa Rahama lakabi da Sizzling Siren, watau “tauraruwa mai walkiya”
Wannan fitacciyar ‘yar wasan ta Kannywood, wacce kuma ta fara fitowa a fina-finan kudancin Najeriya, Nollywood, tana da mabiya sama da 249,000 a Instagram, yayin da fiye da mutum 47,000 ke bin ta a Twitter.
Rahama, wacce ake yi wa lakabi da Sizzling Siren, watau “Tauraruwa mai Walkiya”, ta fara fitowa a wani fim mai suna ‘Gani Ga Wane’, kuma tun daga lokacin tauraruwarta ke haskakawa a Kannywood, inda yanzu take cikin manyan ‘yan fim din da ake ji da su.