Bamu samu kudi a gidan Lawan Daura ba -Inji hukumar EFCC

 

Mukaddashin shugaban kasar ya yi tir da aikin da ya bayyana cewa ya ci karo da tsarin mulkin Najeriya tare da shan alwashin ganowa da hukunta wadanda ke da hannu a aikin.

Da yammacin ranar ne dai Osinbajo ya gana da sabon shugaban hukumar da ya maye Daura, Matthew B. Seiyefa, da kuma shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon gasa, Ibrahim Magu.

Washe gari dai rahotanni sun ce jami’an hukumar EFCC sun kai samame gidan tsohon shugaban hukumar DSS, Ita Ekpeyong.

Bayan nan kuma aka fara yada wani bidiyo a shafukan sada zumunta wanda ake ikirarin cewar bidiyon kudin da aka samu a gidajen Tsohon shugaban DSS, Lawal Daura ne.

Sai dai kuma binciken BBC ya gano cewar wannan bidiyon na kudaden da EFCC ta gano ne a wani gida daga cikin jerin gidaje masu alfarma da ake kira Osborne Towers a unguwar Ikoyi ta Legas.
Kuma a cikin watan Afrilun shekarar 2017 ne EFCC ta yi aikin wanda a yanzu ake ci gaba da yada bidiyon.

Bayan haka kuma hukumar DSS ta fitar da wata sanarwa inda ta ce bidiyon ba na gidan stohon shugabanta bane.

Hakzalika, sanarwar da kakkin hukumar DSS, Tony Opuiyo, ya fitar, ta ce ba gaskiya ba ne cewar an sami tsabar kudi Naira biliyan 21 da bindigogi 400 da kuma dubban katunan zabe na din-din-din a gidan Daura.

Yada labaran karya yazama ruwan dare aduniya.

Source: https://ift.tt/2PcK783

Leave A Reply

Your email address will not be published.