Banida niyyar zama shugaban majalisa -Inji Godwils Akpabio

Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar Godwils Akpabio yace bashida niyyar zama shugaban majalisar dattawa ayanzu.

A ranar laraba ne Senata Godwils ya sanarda fitarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. A cewarsa ya bar jam’iyyar PDP ne don cigaban alummar Nigeria.

Akpabio yace ” Banida niyyar zama shugaban majalisar dattawa a yau, amma inada burin zama duk abinda ubangiji yakeso inzama. Suna Godwill saboda haka na yarda da ikon ubangiji.

Da ake tambayarsa me zai ce idan har APC ta fadi zabe a 2019. Sai yace” Mutane suna bani mamaki saboda yadda suka dauka cin zabe shine nasara a’a bahaka bane, Yin aiki da damarda kakeda ita shine nasara koda ka fadi zabe idan kayi aiki da damarka ta baya to nasara kayi, Mafi yawan masu son cin zabe sune masu yin magudin zabe.

Senata Akpabio shine senata daya cika shafukan sada zumunta saboda komawarsa APC.

Source: https://ift.tt/2M3USvD

Leave A Reply

Your email address will not be published.