Barawo Ya Sace Wayar Tsohon Gwamnan Jihar Neja A Masallaci

Wata karamar kotun birnin tarayya ta yanke ma wani mutum mai suna Muhammad Umar zaman gidan kaso kan aikata laifin satar wayar tsohon gwamna jihar Neja Babangida Aliyu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito an kama mai laifin ne a Kwamba dake karamar hukumar Suleja yankin jihar Neja.

An yanke ma Umar zaman gidan yari wata daya kamar yadda sashi na 287 na kundin ka’idojin ladabtarwa ya tanadar. Dan sanda mai kara AZ Dalhatu ya bayyana cewa wanda ake zargin ya saci waya kirar Samsung galaxy daga aljihun tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu a masallacin An-Nur dake unguwar wuse II a Abuja a yayin sallar juma’a. ya kara da cewa amma an kwato wayar daga hannun barawon.

Da aka karanto ma wanda ake zargin laifin nasa, ya amsa laifinsa daga nan sai Alkali Sadiq Abubakar ya yanke masa zaman gidan kaso na tsawon wata guda, ko kuma ya biya tarar naira dubu biyar (5000).

A wani labarin kuma, ita dai kotun Alkali Sadiq Abubakar ta saurari karar da aka shigar kan wani Adamu Asaph da laifin satar kwalayen kwaroron roba guda biyu da darajar su ta kai N3000.

Dan sanda mai kara yace kwaroron robar mallakan hukumar kula da lafiyar al’umma ce. An gurfanar da Asaph ne a karkashin sashi na 289 na kundin ka’idan ladabtarwa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.