Barayin Nigeria Baza Suyi Barci Cikin Dadi Ba Inji Baba Buhari

Barayin Nigeria Baza Suyi Barci Cikin Dadi Ba

Barayin Kudin Nijeriya Ba Za Su Yi Bacci Cikin Dadi Ba, Inji Shugaba Buhari

Daga Sani Twoeffect Yawuri

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk wanda aka samu da cin hanci da rashawa ko kuma wawashe dukiyar kasa ba za su samu damar yin barci cikin dadi ba saboda irin yadda hukumomin dake yaki da cin hanci da rashawar suke kokari.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a lokacin da ya gana a lokuta daban-daban da shugabannin Darikar Kadiriyya ta Afrika da kuma kungiyar Izala a fadar sa dake Villa a Abuja a jiya.

Shugaban ya kara da gargadi da cewar duk wanda aka samu da cin hanci da rashawa ko wawashe dukiyar kasa to lallai zai fuskanci fushin hukuma. Haka kuma yace za a tabbatar da adalci a yaki da ake yi da cin hancin da rashawar.

Ya kuma bukaci shugabannin addinin da su gargadi mabiyansu da kula da hakkin kowa.

Haka kuma yace wadanda suka sace dukiyar al’umma suka tsare kasashen waje ba za su samu damar morar wannan dukiyar ba, kuma za su tabbatar sun dawo da dukiyoyin kasa Nijeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.