Bikin Ranawar Mawakan Hausa Ta Duniya Daga Aminu Ala

Za A Gudanar Da Bikin Ranawar Mawakan Hausa Na Duniya A Jahar Jigawa Ranar Daya Ga Watan Junairu 2017.

DAGA. .  Mawaki Aminu Ladan Alan Waka.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram , Mawakin ya bayyana wannan rana ta mawakan Hausa na Duniya da cewa.

Rana ce abar Alfahari ga dukkan daukakin Mawakan Hausa ako ina suke a fadin Duniya .

Kuma ya kara da cewa , Rana ce ta Zumunci da kuma kulla kyakykyawar alaka tsakanin mawaka, Kuma ranace ta musharakar Ilimi daga Masana akan harkar Waka da Mawaka ke nunawa Duniya cewa Mawaka sunada Rana a cikin ko wacce Al’umma ba rana irin ta shanyar Gariba.

FITACCEN MAWAKI ADAM A ZANGO KENAN. 

BIKIN RANAR MAWAKAN HAUSA POUNDATION . 
Shidai wannan biki na ranar mawaka, Anfara gudana dashine tun a shekarar 2013.
A inda aka gudanar da taron farko a Jahar Kano , A filin taro na “Garban Gora House dake guda Abdullahi Way Farm Center Kano . 
Inda aka gudanar da taron bisa hadin guiwar wasu daga cikin manyan Malaman sashen nazarin harsunan Nigeria da kimiyyar harshe na Jami’ar Bayero Kano . 
Professor Sa’idu Muhammadu na Gusau da shuga ban sashen Dr. Aliyu Mu’azu Zariya. Tare da wakilcin masarautar Kano karkashin Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Alh: Ado Bayero , Daya Wakilta San Kano Alh: Aminu Ado Bayero . 
Sannan wannan taro ya samu tagomashi da rubutu daga shahararrun masana irinsu Professor Muhammad Sa’idu na Gusau.

Wanda ya gabatar da mukala akan inganci da kuma halascin wannan rana ta Mawakan Hausa , tare da ingantaccen tsari ta yadda za’a kyautata gudanar da wannan biki yadda abin zai samu karbuwa da daidaito da Shari’a da Al’ada.

Sannan shi kuma Wanban Kano Alh : Aminu Ado Bayero, ya kadamar da wannan rana ta daya ga watan Junairu a matsayin Ranar Mawakan Hausa Ta Duniya baki daya. 

FITACCIYAR WAKAKIYA ZAINAB BADALI KENAN. 

Za A sake gudanar da wani gagarumin bikin ne a ranar 1 ga watan Junairun 2017 a Garin Dutse babban Birnin Jahar Jigawa . 

Leave A Reply

Your email address will not be published.