Budurwa Ta Kai Mahaifin Ta Kara Kotu Saboda Ya Hana Ta Auren Wanda Ta Ke So

Budurwa Ta Kai Mahaifin Ta Kara Kotu Saboda Ya Hana Ta Auren Wanda Ta Ke So

Khadijat Ibrahim, wata budurwa ce mai Shekaru 23 da ke zaune a Abuja ta kai mahaifin ta Ibrahim Bassa kara kotu saboda ya ki yarda ta auri saurayin da zuciyar ta ke muradi.

Khadijat ta fada wa kotun cewa mahaifinta ya ki ganin saurayin domin a yi maganar aure kuma ya ki ya bata gamsasshen dalilin da ya sa ya yi hakan.

Ta ce saurayin na ta mai suna Abdulhameedu ya sha yin kokarin ganin mahaifin na ta,amma da ya ji zai zo, sai ya bar gidan da gangan.

Ta ci gaba da cewa, dalili daya kawai mahaifin na ta ya bata, kuma shi ne cewar saurayin na ta ba bafulatani ba ne, ita kuwa shi kadai take so.

Budurwar Ta roki kotun da ta tilastawa mahaifin ta da ya bada auren ta ga saurayin, wanda ta ce ta na so har zuciyar ta.

Mahaifin budurwar, Bassa ya shaidawa kotu cewa tabbas ya aikata wadannan abubuwa.

Ya ce ya yi haka ne kuma saboda bai yarda da zabin ‘yar tashi ba.

Ya ce ya sha yi mata gargadi cewa aure ba abun wasa bane.
Toh ta ya ya za ta auri namijin da ba su san asalin shi ba?

Ya ci gaba da cewa, idan bafulatani mutum zai aura, dole sai kowa ya san daga wani tsatso ya fito.

A cewar shi ma “‘yar sa ba ta yi girman daza ta iya zaba wa kanta miji ba, ballantana ta kawo mana wanda bamu san inda ya fito ba

”Ya ce amma ‘yar shi bata jin magana, gashi har ta kai ga ta kawo shi kotu.

Alkalin kotun Abdullahi Baba ya dage sauraran karar zuwa ranar 29 ga watan Mayu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.