Buhari bai Cancanci mulkin nigeria ba tunda nafishi ilimi – Tanimu Turaki

Daya daga cikin masu neman jamiiyyar PDP ta tsaida dan takara a zaben 2019, Kabiru Taninmu Turaki ya shaida cewa yafi shugaba Buhari cancantar mulkin nigeria tunda yafishi ilimi da sanin siyasa. 
Kabiru Turaki wanda babban lauya ne da ke da matasayin SAN, yana daga cikin mutanen da suke fatan karawa da Shugaba Buhari idan APC ta tsayar da shi takarar shugabancin kasa.
Tsohon minista ne a gwamnatin PDP ta Goodluck Jonathan, kuma yana cikin ‘yan jam’iyyar ta PDP da suka kasance a cikinta lokacin da take fama da rikicin shugabanci.
Turaki wanda ya fito daga jihar Kebbi ya ce ba za su samu matsala da sauran masu neman PDP ta tsayar da su takara ba, domin kuwa akwai fahimtar juna tsakaninsu.
Ya ce idan ya samu damar zama shugaban kasa zai yi abubuwa da dama da za su inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Akwai dai wasu gaggan jam’iyyar ta PDP da dama da ke neman takarar shugabancin kasar a zaben na badi.

Source: https://ift.tt/2Aht2Xc

Leave A Reply

Your email address will not be published.