Buhari : Rikicin Buhari da yan majalisa asara ne ga talakawa

Dambarwa tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dattijai ta kara zafafa, bayan gaza bayyanar da ministan shari’ar kasar,

Abubakar Malami ya yi a zauren majalisar wadda ta gayyace shi kan batun karar da ya shigar da sanata Bukola Saraki da Ike Ekwerenmadu bisa zargin yin jabun dokoki.

Ministan dai ya aika wani jami’i ne don ya wakilce shi maimakon zuwa da kansa, lamarin da ya fusata ‘yan majalisar.

Wasu dai na ganin irin wannan dambarwa za ta dauke hankalin gwamnati daga yi wa talakawa aiki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.