Buhari ya tura jami’an tsaro 1000 zuwa jihar Zamfara

Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya bayar da umarni tura jami’an tsaro 1000 ya zuwa jihar Zamfara domin su kawo karshen kashe-kashen dake faruwa a jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar,ya ce jami’an tsaron za su ƙunshi, ƴansanda, sojoji, jami’an Civil Defence da kuma sojojin sama.

Shehu ya ce za a tura jami’an ne domin su fara kai zazzafan hari kan yan bindigar da suka addabi jihar.

Ya kuma ce rundunar sojan saman Najeriya ta tura jirage ya zuwa filin jirgin saman jihar Katsina inda ya fi kusanci da jihar domin kai daukin gaggawa duk lokacin da maharan suka kai hari.

Source: https://ift.tt/2Ao89d6

Leave A Reply

Your email address will not be published.