Ci Gaba Da Yakin Biafra Kashi Na Biyu, Nasarar Sojojin Nigeria

Abubuwan Dasu Kamata Ko Wanne Dan Arewa Ya Sani Game Da Yakin Biafra. Kashi Na Biyu.

Daga : Hamisu Hassan Ahmed

Cigaba da maganar gumurzun yakin Biafara.

wasu mutane suke jawoma kan su da mutanen su mutuwa, sannan su gudu kuma su daura laifin akan wasu.
-bayan rashin yadda da sulhu da Ojukwu yayi,rashin amincwa da jahohin da gwamnati ta kirkiro, tilasta ma kamfanonin Petur da ba bangaren su dukiyar mai,to daganan Gangunan yaki suka fara bugawa.

-acikin watan mayu na 1967 Ojukwu yasanarda kafa sabuwar kasa mai suna Biafara ,wanda har zaku iya ganin yadda aka rantsar da shi amatsayin shugaban kasa.

-shugaban kasa yakubu gowon, yasa dukar tabace da kuma umartar sojoji da dumfarar wurin yan tawaye.

-maman shuwa shine yajagoranci runduna ta farko domin kutsawa Enugu wadda itace babban birnin biafara.zamui magana kan wannan jarumi wani lokaci akan cewa: shin mutwar shi ramuwar gayyace wasu sukayi koko Boko Haram ne?

-da su Ojukwu sukaga ana kokarin shiga wurin su, sai suka fadada yakin suka tsallaka kogin Niger zuwa garuruwan Yaroba kamar su Benin saboda:

-kada sojojin gwamnati sui amfani da garuruwan wurin kai musu hari.
-kuma su yaudari yaroba dacewa:kuzo mu yaki hausa fulani saboda makiyan mu ne baki daya, arzikin da muke dashi damu da kune,shiyasa muna neman goyan bayan ku.

-Ojukwu ya mallaki makamai kai harda jiragen yaki wanda kasashe irin su potugal,france, Afria ta kudu ke turomai,zamuji manufar kowace kasa akan haka.

-Murtala Muhamnada ya jagoranci runduna ta 2, wanda kuma shine ya wargaza sojojin Biafara wanda suka tsallakka kogin Niger wanda suka kwashi kashin su ahannu.

zakaji suna fadin wai yai kisan kiya shi agarin Asaba,wanda duk mai fahimta yasan siyasar wanda baiyi narar yaki bane da kuma sakama mutane kin shine, saboda duk wanda kaga ankashe ,to fafatawa akai da shi.kuma kowa yasan Ojukwu yaba yara da mata makamai domin ya tura su zuwaga hallaka.

-Benjamin Adekunle (balack scorpion)yajagoranci runduna ta 3 A 1968 ,wanda yafara tarwatsa yan tawaye ta garin Bonny wanda yake garin Rivers ayanzu.

-gumurzu yaci gaba wanda Har Allah yaba sojan Nigeria nasarar kwace Enugu awatan OCTORBER 1967, hakan sai yasa yan tawaye suka maida babban birnin nasu zuwa Umuahia.

-ataikacedai a 1968 sojoji suka kwace Umuahia ,daganan fa sai akaima yan tawaye kofar rago, yaki yakara cigaba sai babban birnin karyar yakara komawa garin Owerri.

-acikin shekara ta 1970 wuta tai wuta ,sai sojan Nigeria suka kwace Owrri da filin jigin sama.

-Ojukwu yagudu zuwa kasar Ivory Coast bayan yai sanadiyar mutuwar fiyeda milian daya da yunwa da ciwuka.

-Phillip Effiong yamika wuya daceawa sunyi saranda wanda Obasenjo  ya bayyana hakan.

wannan tarihin munsan kowa yasan shi ,amma muna sone mu tattauna akan:
manufofin wasu kasashe masu jawo mana yaki saboda bukatar su.zamuji dalilin su.

Meyasa Ojukwu yanemi ai tsarin Confederation akan tsarin da muke kan shi?nan gaba zamuji.

abun nada yawa yan uwa ,amma zamu dan tabo abunda mukai alkawari abayani masu zuwa insha Allah.

® www.HausaMedia.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.