Da Alama Za’a Iya Gano Wadanda Suka Kashe Sheikh Jafar.

sheikh Jafar mahmud Adam Kano

A Nigeria, wasu Malaman addinin Musulunci sun kalubalanci rundunar ‘yan sandan kasar da ta fito ta yi wa al’umma cikakken bayani game da binciken da suke yi na wadanda suka hallaka fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Ja’afar Adam.

Daya daga cikin malaman musulunci a kasar nan, Sheikh Aliyu Muhammad ya ce hakan ya zama wajibi sakamakon rudanin da ya biyo bayan sanarwar da rundunar ta yi bayan samame da jami’anta suka kai gidan Sanata Danjuma Goje a makon da ya gabata.

‘Yan sandan dai sun ce daga cikin abubuwan da suka samu a gidan Gojen har da wani fayil da ke nuna yadda tsohon Gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya kitsa kisan da aka yi wa Sheikh Ja’afar.

® Oak Tv Hausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.