Dabarun Kirkiro Sana’a Da Aiyukan Yi, Da Kuma Farfado Da Tattalin Arzikin Arewa Kashi Na 3

Dabarun: Kirkiro Sana’a Da Aiyukan yi Da Kuma Farfado Da Tattalin Arzikin Arewa…. Chef BNG Bashir Ibrahim Na’iya.

Waiwaye

A wancen rubutun wanda nayi akan “inventors” nayi bayanin dabarun kirkiro sana’a, duk da dai na san watakila hanyoyin dana kawo su yi wasu tsauri, domin na sha yanzu magani yanzu bane, dole sai an yi zurzurfan tunanin kirkiro sana’a ta hanyar magance wata matsala, ko kuma kirkiro sana’a ta hanyar saukaka wani da a da ake yinsa a wahalce, kuma dai kirkiro sana’a ta hanyar zamanantarwa ko inganta packaging, hanyoyin dai suna da yawa, ga wadanda basu sani ba to ga shi na bude musu kofa, sai a shiga rumbun nazari da bincike. A yau kuma zan yi bayani ne akan:

Investors/masu zuba jari.

Allah ya kawo mu wani lokaci wanda masu kudin da marasa kudin kowa kuka yake yi. Domin idan a karshen shekarar 2016 kana da jarin naira miliyan goma, ko kuwa kudin ne da kai a  ajiye, to a farkon shekaran nan ta 2017 sun ruguje sun dawo kasa da miliyan biyar. Shi yasa a gaskiya ajiye kudi ba tare da ana juya su ba, wani lokacin yin hakan ba dabara bace. Idan kuma kana takama ka sayi filaye ko gidaje, to sai sanda ka tashi sayarwa ne za ka sha mamaki musamman a wannan yanayin. Saboda haka ni a ganina babbar mafita ita ce “Investment”, dayawa na ga mutane suna amfani da sunan investment akan harkokinsu ba tare da suna yin investing din komai ba. Amma me ake nufi ne da Investment din?

Investment

Ni a fahimtata investment shi ne, idan kana da kudi, to ka tura kudin su je su yi maka aiki su nemo maka wasu kudin shi ne ma’anar investment. Akwai hanyoyi da dama da mutum zai iya yin investing din kudinsa, amma anan ni ina magana ne akan abin da ya danganci sana’a/kasuwanci dss. ba sayen gidaje ko gonaki da filaye nake magana ba.

A kasashen da su ka ci gaba, idan ka kirkiro wata sana’a kuma ya kasance abubuwan da kake yi sun karbu a wajen jama’a, za ka iya zuwa wajen investors ka yi musu bayani, idan sun gamsu kuma suna da sha’awa, sai ku yi yarjejeniya akan yadda za ku raba ribar, sai su zuba jarinsu, amma kafin su investors zuba kudinsu sai sun auna sun ga har tsawon yaushe ne zai dauka kafin kudin da za su zuba su dawo? Sannan su za taimaka ko kamfanin  da hanyoyin da sana’ar zata kara habaka, hakan zai sa mutane da dama su sami aiyukan yi. To hakika irin wannan investors na ke yi mana kwadayin a ce muna dasu a Arewa daga cikin masu kudinmu. Domin akwai dayawa wadanda suke da hikimar kirkiro sana’o’in da za su samar da aiyukan yi, amma kuma basu da jarin da za su yi sana’ar. Sai dai hakan bazai zama uzurin da zai haifar da zaman banza da kuma mutuwar zuciya ba saboda rashin jari, domin kuwa akwai da dama wadanda su ka fara sana’a ba tare da wani jari mai karfi ba yanzu haka sun zama masu kudi, kuma har sun samar da aiyukan yi ga dumbin matasanmu, InshaAllah zan kawo misali a rubutuna na gaba kuma na karshe akan ENTREPRENEURS.  

Matsalar kawai ita ce, yanzu cin amana da rashin gaskiya da cuta sun yi mana yawa, amma sai dai duk lalacewar zamani ba a rasa na Allah, masu gaskiya da rukon amana.

Chef Bag 05/08/17.

© www.HausaMedia.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.