Dabarun: Kirkiro Sana’a Da Aiyukan yi Da Kuma Farfado Da Tattalin Arzikin Arewa.

Dabarun: Kirkiro Sana’a Da Aiyukan yi Da Kuma Farfado Da Tattalin Arzikin Arewa…. Chef BNG

Gabatarwa

Tun kwanaki na so fara wannan rubutun mai muhimmanci wanda kusan yafi kowanne rubuta dana yi a baya, amma sai na lura duk hankulanmu sun fi karkata ga abubuwan da suke faruwa, yau a ce wannan gobe kuma a ce wancen, ganin cewa abun ba na kare bane, sai kawai na yanke na fara rubutun a yau Juma’atu babbar rana.

A zahirin gaskiya duk da cewa ba a Najeriya nake ba, amma idan na ga duk wani abun ci gaba, sai zuciya ta dinga riyamin yadda abun zai kasance a kasashenmu. Ni ba ma’abocin jin ko kallon labarai bane, domin tunda aka gama yin zaben Trump da Hillary ban sake waiwayar tashar CNN ba. Tashar dana ke kallo kullum ita ce tashar Business wato CNBC, akwai shirye-shirye na musamman akan business da kullum basa wuce ni, kai! ko sun wuce ni to zan hau internet na kalla.

Yawan kallon shirin dana ke yi, yasa na fahimci abubuwa da daman gaske. Na fahimci dabarun yadda ake kirkiro sana’a wanda hakan ne yake haifar da samun aiyukan yi da kuma dogaro da kai, wadannan abubuwan ne suke taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin kasa, shi kuwa gyaruwar tattalin arziki yana rage fatara da yunwa, sannan kuma idan kowa yana da abun yi to dole manyan laifuka irin sace-sace da fashi da makami da kuma fadace-fadace sakamakon zaman banza, duk za su ragu sosai da sosai.

In har muna son Arewa ta ci gaba a fagen kirkiro sana’o’in dogaro da kai da samar da aiyukan yi da kuma farfado da tatattalin arzikin yankinmu, to a gaskiya dole sai mun kwaikwayi yadda duk kasasehen da su ka ci gaba suke yi, to sannan ne za mu sami wannan ci gaban. To in kuwa haka ne, akwai bukatar mu fahimci abubuwa guda uku:

Inventors/masu hikimar kirkira
Investors/masu zuba jari
Entrepreneurs/masu kirkirar businesss

InshaAllah a posts dina na gaba zan dauki kowanne nayi bayani dalla-dalla, in har za ku jure bibiyata, to ina tabbatar muku, InshaAllah a karshe za ku sami wani ginanne tunanin ciyar da kanku gaba ta fannoni da dama wajen kirkiro sana’a. Masu yimin inbox akan na taimaka musu da yadda za su kirkiro sana’a to ga fa dama ta samu a b’agas. lol

Allah yasa mu dace.

Chef BNag 04/28/17

Da Fatan Zakuci Gaba Da Kasancewa Da Shafin HausaMedia, Insha Allah Zamu Ci Gaba Da Kawo Muku Wannan Shirin Daga Nan Har Illa Masha Allah.

® Bashir Ibrahim Na’iya

Leave A Reply

Your email address will not be published.