Dabarun: Kirkiro Sana’a Da Aiyukan yi Da Kuma Tattalin Arzikin Arewa Darasi Na 1.

Dabarun: Kirkiro Sana'a Da Aiyukan yi Da Kuma Farfado Da Tattalin Arzikin Arewa

Dabarun: Kirkiro Sana’a Da Aiyukan yi Da Kuma Farfado Da Tattalin Arzikin Arewa…. Chef BNG

Inventors/Masu hikimar kirkira

A kasashen da su ka ci gaba, na lura da kyau, inventors suna amfani ne da dabaru da daman gaske wajen kirkiro wani abu wanda zai magancewa mutane wata matsala, ko kuma su kirkiro wani abu wanda zai saukakawa mutane fiye da yadda suke yin abun a da. Wasu kuma package/mazubi suke kirkirowa wanda zai ja hankalin mutane su ji suna son abun, akwai dai hanyoyi da dama na kirkiro sana’a.

Ba mamaki wasu za su ga wannan dan bayanin kamar ba wani abu bane da za a darar a gaba. Amma Wallahi kun ji na rantse muku, ni gau ne, inventors a kasashen da su ka ci gaba dabarun da suke bi kenan na kirkiro abubuwa, sannan ni ma shaida ne, domin hoton da kuke gani cake dina ne, a 2014 duk wani store ko bakery da ake sayar da cake sai da na je a Kano na ga irin package din da suke yi wa cake dinsu, hakan ya bani damar kirkiro nawa package din wanda ya sha bamban dana kowa. Waje daya tilo dana samu suke karbar cake din, abin da manajan ya fara gayamin cewa ya yi, zan karba ne kawai saboda bamu da irin wannan samfur din, kun ga ko anan kirkira tayi rana kenan, sai nayi sawu uku ina kai cake din yana karewa, amma na sauran gama garin cake din ko kallonsa ba a yi.

Idan muka koma kan batun matsaloli, hakika a kasashenmu akwai matsaloli masu yawan gaske, dogon tunani da bincike za su kaimu ga kirkiro sana’o’in da za su zame mana mafita daga matsalolin. Sai dai matsalarmu gajen jakuri, mun fi son sha yanzu magani yanzu. Akwai misalai da dama dana ke son kawo muku, amma matsalar wasu za su iya cewa, ai bazan hada Najeriya da kasashen da su ka ci gaba ba. Amma na tabbata ko a Najeriya akwai dayawa wadanda suke yin amfani da wadannan dabarun wajen kirkiro sana’a. Misali daya dazan baku shi ne, wani babban Malami a Jami’ar Bayero Professor Ali Muhammad Garba, ganin yadda ake fama da matsalar ruwa, sai ya yi wani rubutu mai muhimmanci akan yadda za a iya kirkiro sana’ar sayar da ruwa ta hanyar yin amfani da babur din adaidaita sawu maimakon kurar ruwa, domin babur din shima zai iya shiga loko-loko, sak’o-sak’o kuma ya fi kurar ruwa sauri nesa ba kusa ba.

Irin wannan tunanin ne nake so na ga matasanmu sun sa a ransu, domin shi ne kadai hanyar da za mu ci gaba, amma muddin za mu tsaya cacar baki da hirar ball, to tabbas za a barmu a baya sosai da sosai. Kowa da irin baiwar da Allah yai masa, wani ba shi da kudi, amma kuma Allah ya bashi hikimar kirkira, wani kuma yana da kudin, amma kuma bashi da lokacin zaman tunanin kirkiro wani abu. Saboda haka kun kenan ga mai hikimar kirkira ga kuma mai kudi, saboda haka sai su hadu kenan su hada karfi da karfe a cikin rubutuna na gaba akan Investor/masu zuba jari.

Allah yasa mu dace, ameen.

Chef BNG 05/02/17

® Bashir Abubakar Na’iya

Leave A Reply

Your email address will not be published.