Daliinda yasa bazan sauka daga mukamina ba -Inji Bakola Saraki

Shugaban majlisar dattawan Nigeria Bokala Saraki ya bayyana cewa bazai amince da kiran da ake masa ya sauka daga mukaminsa ba har sai wadanda suka zabeshi sun nuna rashin goyon bayansu ga cigaba da mulkinsa.

Saraki ya bayyana haka ne a ayau laraba lokacinda yake zantawa da manema labarai  a birnin tarayya Abuja.

Tun dai lokacinda Saraki ya bar jam’iyyar APC shugabanin jam’iyyar keta kiran ya sauka daga mukaminsa tunda jam’iyyar daya koma PDP batada rinjaye a majalisar.

A martanin daya mayarwa jam’iyyar  APC, Saraki yace zai cigaba da zama a mukaminsa idan har senatocin majalisar sunajin dadin zamansa tunda sune suka zabeshi.

Saraki yace ” Taya zan sauka daga mukamina kawai don wasu sunaso in sauka. Idan nai haka na karya kwarin gwiwar jama’arda suke goyon bayana. zan sauka cikin lumana idan har sanatoci suka kada kuri’ar rashin goyon bayana.

Saraki ya kuma kira ‘yan Nigeria da kar su yarda da batutuwanda ake magana akan cewa shi mai son mulki ne kota halin yaya.

Speaker Yakubu Dogara ne a gefen Saraki lokacinda ake hira dashi saidai Dogara bai ce uffan ba har aka gama hirar.

Source: Premium timesNG

Source: https://ift.tt/2Mu7GYg

Leave A Reply

Your email address will not be published.