Dalilan Da Suka Sa Na Kafa Sojojin Biafra Na Sirri – Nmandi Kanu

Nmandi Kanu

Dalilan Da Suka Sa Na Kafa Sojojin Biafra Na Sirri – Nmandi Kanu

Nnamdi Kanu ya zargi gwamnati kan rashin kare yan kudu maso gabas Yace karda mutane su razana a kan ayyukan da IPOB zata kaddamar

Shugaban IPOB din yace an kafa sojojin Biyafara ne don kare hakkin mutanen Shugaban IPOB Nnamdi Kanu yace ya kaddamar da sojojin Biyafara ne saboda samar da tsaro ga yan kabilar Igbo.

Kanu yayi magana ne jim kadan bayan ziyarar da ya kai wa sanata Enyinna Abaribe a Abia, a ranar Talata 22 ga watan Agusta.

Shugaban Biyafaran ya zargi gwamnatin tarayya da rashin kare hakkin yan kabilar Igbo, hakan yasa ya shirya sojojin Biyafaran.

Yace yan sanda sun gaza hukunta Fulani makiyaya masu kasha yan Igbo. Sanata Abaribe ya bayyana cewa IPOB ta tabbatar da cigaba da zaman lafiya.Ya kara da cewa hadin kan yan Najeriya dole ne tunda hakan ne zai tabbatar da zama cikin kwanciyar hankali.

Yayi kira ga yan Najeriya da su ci gaba da aiki kan zaman lafiya sannan majalisar dattawa zata ci gaba da tattaunawa a kan al’amarin. Bayan haka, Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci shuwagabannin tsaro da su magance jami’an IPOB na sirri da Boko Haram da duk ta’addanci a kasar.

Vanguard ta rahoto cewa, Shugaban ma’aikatan tsaro, Abayomi Olonisakin, ya bayyana cewa a kan al’amarin ne shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shuwagabannin tsaro.

Leave A Reply

Your email address will not be published.