Dalilinda yasa bandamu da masu ficewa daga APC ba -Inji Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa dalilinda yasa bai damu da masu ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki ba shine saboda yanada tabbacin talakawan Nigeria sun amince da mulkinsa.

Buhari ya bayyana hakan ne a birinin LOME  yayin wata ziyara da yakai kasar Togo a ranar 29 july, 2018. Ina yace talakawan Nigeria su zasu bada amsa da kariyar Gomnatinsa.

Da yake ansawa manema labarai tambayoyi akan yadda ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki suke ficewa zuwa PDP sai Yace ” Ni banda damuwa akan masu sauya sheka saboda mafi ‘yan nigeria sun yarda da tafiyar mulkinmu kuma su suke karemu da gamsassun amsoshi akoina sun yarda damu kasancewar sunga irin kokarin da muke akansu.

Sannan Buhari ya yabawa ‘yan nigeria wadanda suka taho daga yankuna da sassan kasar togo domin tarbarsa ya kuma gode musu da yadda suka nuna alfahari da mulkinsa.

Bayanin ya fito ne daga ofishin babban mai bada taimakawa shugaba Buhari a fannin yada labarai. Mallam Garba Shehu. Yace haryanzu wannan gomnati tanada karfi da kima a idon talakawa saboda yadda suka dukufa wajen samarda tsaro, lafiya, da dukkan abubuwan cigaban alumma.

Source: https://ift.tt/2OrUsNf

Leave A Reply

Your email address will not be published.