Dawayya tayi Kaca-kaca da abokiyar san’arta

Dawayya
Tsohuwar Jarumar kannywood wadda kuma har yanzu ake damawa da ita Rukayya Umar Santa wadda aka fi sani da Rukayya Dawayya ta yiwa abokiyar san’arta kashedi a shafinta na Instagram,

Ta bayyana cewa duk wadda ta shigo fim daga shekara 10 zuwa yanzu su ta gani suna birgeta yasa itama ta shigo,

Duk dai  bata kira sunan kowa ba amma Wannan ba sabon abu bane ga Jaruman kannywood na huce haushi a shafukan sada zumunta musamman Instagram. Duk da wannan zafi da ta dauka Jarumar a karshe ta bawa masoyanta Hakuri.

Jarumar  Wadda aurenta ya mutu a kwankin baya  ta fara fitowa a fina-finan kannywood fiye da shekara goma da suka wuce a wani shiri mai suna Dawayya.

Ga dai cikakken abunda Jarumar ta rubuta.

” Bude idonki sosai ki ganni. karyane kice kina masana antar kannywood baki sanni bah. kokice bakisan sunana bah wlh karya kike. daga 10 years zuwa yanzu duk wacce ta shigo industry mutagani tashigo. idan kinzo da Alkhairi  kiga Alkhairi idan kinshigo da sharri ko kwadayi duk kigani a kwaryar shanki. karyar banza. sorry my fan’s wata banzace tabani haushi.  “

Source: https://ift.tt/2Bf7ICj

Leave A Reply

Your email address will not be published.