EFCC Na Neman Wata ‘Yar Damfara A Atm Hattara Jama’ a

EFCC Na Neman Wata ‘Yar Damfara A Atm Hattara Jama’ a

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta baza komarta domin gano wata mace da ke damfarar mutane a injin cirar kudi.

Wata sanarwa da kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya fitar ta ce matar, mai suna Akinade Tofunmi, tana zuwa wurin cirar kudin ne da zummar taimakon mutanen da ke son cirar kudin amma sai ta sace bayanan katin cirar kudin sannan ta sace kudinsu.

EFCC ta kara da cewa matar ta sace fiye da Naira miliyan uku cikin kwana daya.

A cewar hukumar, Akinade ta gamu da wata mata a wani wajen cirar kudi a birnin Ibadan, inda ta nemi ta taimaka mata wajen cire kudi bayan da ta gano cewa tana fuskantar matsala wajen cire su.

Hakan ya ba ta damar sanin lambar sirrin katin cirar kudin matar, kuma da ta tashi bai wa matar katin cirar kudin, sai kawai ta ba ta na jabu, ita kuma ta rike na matar.

EFCC ta ce Akinade ta shafe daren ranar tana cire kudi daga asusun matar, kuma da gari ya waye ta ci gaba da cirewa.

Hukumar ta EFCC ta bukaci jama’a da su sanar da hukumomin tsaro da zarar sun ganta, tana mai gargadin mutane da su kula da mutanen da ke tsayawa kusa da su idan suka je cirar kudi a na’urar ATM.

Leave A Reply

Your email address will not be published.