EFCC Ta Gurfanar Da Wasu Mutane Bisa Kwarmata Bayanan Da Ba Na Gaskiya Ba

EFCC Ta Gurfanar Da Wasu Mutane Bisa Kwarmata Bayanan Da Ba Na Gaskiya

EFCC Ta Gurfanar Da Wasu Mutane Bisa Kwarmata Bayanan Da Ba Na Gaskiya

Daga Habu Dan Sarki

Hukumar yaki da almundahanar kudade ta EFCC ta kama wasu mutane 2 tare da gurfanar da su gaban babbar kotun tarayya dake Maiduguri bisa zargin sun tsegunta mata labarin da ba na gaskiya ba.

A wata takardar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun babban jami’in da ke kula da harkokin watsa labarai da sadarwa na hukumar Mista Wilson Uwujaren, an bayyana mutanen sun bayar da labarin cewa wani mai suna Ba’a Lawal ya binne wasu makudan kudade a cikin gidan sa dake rukunin gidaje na Pompamari.

Amma, a cewar sanarwar bayan jami’an ta sun kai samame gidan an bincika duk inda ake zargi ba a ga wani makamancin zargin da aka yi ba. Don haka ta kama mutanen da suka kwarmata mata bayanan sirrin da ba na gaskiya ba.

Menene ra’ayinku game da wannan mataki da hukumar ta dauka ga masu samar mata da bayanai? Anya kuwa babu wata baraka da aka samu a tsakanin jami’an hukumar?

® Zuma Times Hausa
© www.HausaMedia.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.