Facebook Na Kaddamar Da Toron Inganta Shafi Me Suna “F8”

 Facebook F8

Kamfanin shafin Facebook, na kaddamar da wani taron karama juna sani, mai taken F8.

An shirya taron da zummar kara fitowa da wasu sabbabin hanyoyi da za’a inganta shafin zumuntar na facebook.

Mahalarta taron sun fito daga ko’ina a fadin duniya, don zakulo basirar da Allah, yayi ma matasa a kowane fanni. Kamfanin na facebook na fukantar kalubale daban-daban, daga sauran abokan gogayyar shi.

Kamar su kamfanin Twitter, Instagram, da sauran shafufukan sada da zumunci a duniya. Musamman idan akayi maganar sada zumunci a duniya. Ana kuma sa ran duk a wajen taron kamfanin na facebook zasu kaddamar da wasu sababbin manhajojin su.

Duk wannan yunkurin nasu na maida hankali ne,wajen inganta shafin, da bama mutane damar bunkasa kasuwancisu, ta hanyar amfani da shafin facebook. Mahalarta taron zasu hadu a babban birnin San Jose, a jihar California ta Amurka.

Mahalarta, zasu samu damar haduwa ido-da-ido da shugaban kamfanin Mark Zuckerberg, wanda zai bayyana musu babban kalubale dake gaban su, kamun su dukufa wajen samo mafiti cikin kankanin lokaci, da yunkurin karo yawan abokan hurdarsu.

© Dandalinvoa

Leave A Reply

Your email address will not be published.