Falalu A Dorayi Ya Sake Yin Kira Ga Ma’abota Kallon Fina Finan Hausa

AN YI KIRA DA A KAUCE WA SIYAN FINAFINAN SATAR FASAHA

Shahararran Daraktan finafinan Hausa Falalu A. Dorayi, ya yi kira da masoya kallon finafinai da su kaucewa siyan duk wani fim da alamu suka bayyana cewa an fitar da shi ne ta barauniyar hanya.

Dorayi ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi a manema labarai a shirye-shiryen fitar sabon fim Kamfaminsa mai suna BASAJA. Inda ya ce hakan sabawa doka ne karara barayin ke yi, saboda haka ‘yan kallo su kaurace wa irin wadannan finafinai.

Ya ce finafinan da ainahin Kamfanin fim yake fitarwa su ne na kwarai, domin ana tabbatar da cewa an yi amfani da sinadaran da fim zai yi kal-kal, sabanin na masu satar fasaha, wanda yake fitowa dishi-dishi, kuma likitoci sun tabbatar fa cewa yana da illa ga idanun dan’adam.

Falalu ya kara da cewa “idan har za a rika kashe milyoyin kudi wajen shirya fim, bai kamata ‘yan kallo su biye wa barayin zaune ba, wadanda ke amfani da su don cimma burinsu na satar fasaha.”

Ya kuma karfafa guiwa ga ‘yan kallo kan su kalli fim din BASAJA, domin yana dauke da sako, salo, sahihiyar ma’ana da zai birge kowa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.