Filin Girke Girke Yadda Ake Hada Dambun Kuskus Mai Dadin Gaske

Dambun Kuskus

ABUBUWAN DA AKE BUKATA :-

•Cous Cous
•Nama/Hanta
•Maggi,gishiri
•Green beans
•Albasa, tarugu

MATAKIN FARKO :-

Ki tafasa nama ki sa ruwa da dan yawa, in ya dahu, ki yanka shi ‘kanana, duk kayan hadinki ki yanka su ‘kanana, sai ki juye ruwan naman akan Cous cous, ki sa maggi, curry, gishiri ki juya sosai kisa murfi ki barshi zuwa 5mnt,

Sai ki ‘dauko tukunya ki dora a wuta ki zuba Cous Cous kisa leda ki rufe kamar yadda ake dambun tsaki, 5mnt sai ki kwashe Cous cous din kisa duk kayan hadin da mai ki juya sosai ki Mayar a wuta zuwa minti 3 ki sauke.

Kuma zaki iya sa ganyen alayyaho idan kina bukata. Yana da dadi sosai.

1 Comment
  1. Muhammad Abba Gana says

    :-d

Leave A Reply

Your email address will not be published.