Filin Girke Girke Yadda Ake Hada Wainar Madara Mai Dadin Gaske

Ita dai wannan masar ana iya cinta da miyar kabeji ko Alayyaho kuma zaki iya cinta haka,

Abubuwan Da Ake Bukata

1= Farar Shinkafa
2= Madara gari
3= yeas
4= Bakar hoda
5= Kwakwa
6= Gishiri
7= sugar
8= fulebo na Kwakwa
9= Ruwan kwakwa

Da Farko Saiki jika farar shinkafan ki ta kwana, sai ki nika ta washe gari.

bayan kin nika shinkafar ki sai ki zuba yis sai ki saka shi a rana ya yi kamar awa biyu.

Sannan sai ki dauko shi ki zuba ruwan kwakwa kisa ki kawo madarar garin ki saka sai ki kawo suger kisa sai ki kawo Bakar hoda kisa sai ki juya ya juyu sosai.

Shikenan Saiki Dauko Kaskonki Ki Fara Suya .

Daga Maman Ummi .

Leave A Reply

Your email address will not be published.