Filin Girke Girke Yadda Ake Hada Wainar Semovita

Wainar Semovita tana da matukar kama da Wainar masa. Banbancin su kawai shine wainar Semo ta fi laushi kuma ta fi saukin hadawa, tunda ita ba sai kin jika komai ba kuma ba sai kin yi markade ba. Amma banda wannan, kusan komai iri daya ne. Ga yadda ake hadawa:

Abin da zaki nema

1. Garin Samobita (Semovita)

2. Yis (Yeast)

3. Sikari

4. Gishiri

5. Albasa

6. Man gyada

7. Ruwan dumi

Yadda ake hada wa

1. Da farko zaki zuba garin semovitan ki daidai misali a cikin kwano mai fadi

2. Sai ki zuba yeast da sikari da gishiri daidai misali, kamar dai yadda zaki zuba idan wainar ta shinkafa ce

3. Sai ki kawo ruwan dumin ki ki zuba kina juyawa da muciya a hankali har sai kwabin yayi dai dai da waina. Ruwan dumin yana taimakawa kullin wajen tashi da wuri. Amma idan akwai rana sosai zaki iya kwabawa da ruwan sanyi

4. Sai ki ta juya kullin da muciya har na tsahon minti 15. Idan yayi za kiga yayi mulmul yana kanshi

5. Sai ki rufe shi ki bar shi a rana har sai ya tashi

6. Idan ya tashi sai ki yanka albasa ki soya shi da mai a tanda ko kuma kaskon tuya (Frying pan)

7. Za ki ganta tayi washar kamar wainar shinkafa

8. A na ci da miyar taushe ko miyar gyada ko romon naman kai

DAGA SHAFIN : Alummata.

Leave A Reply

Your email address will not be published.