Filin Girke Girke Yadda Ake Yin Alalan Shinkafa.

 Alalan Shinkafa

Kamar yadda aka san ana yin alale da wake, toh za a iya yi ma da shinkafa kuma ya fito sumul kamar da waken aka yi shi. Akwai Hanyoyi biyu da ake sarrafa wa. Zan zayyano kowanne ba tare da bata lokaci ba.
Kayan hadi
  • Shinkafar tuwo
  • Attaruhu
  • Albasa
  • Gishiri
  • Magi
  • Mangyada hade da manja
  • Kwai
Hanya ta daya
1. Za a jika shinkafar tuwo kamar gwangwani biyu da daddare ya kwana
2. A dafa wata shinkafar daban kamar rabin gwangwani
3. A hada jikakkiyar shinkafa da dafaffiya da attaruhu da albasa a markada
4. A dafa kwai a bare a yayyanka sannan a ajiye a gefe
5. A zuba kayan hadi kamar su gishiri da magi da mai a juya sosai. Sai a fara kullawa a leda ana Jefa kwan, ko kuma a zuba shi a gwangwani a turara.
Hanya ta biyu
1. A wanke shinkafar tuwon a shanya ta ta bushe sai a nika ta.
2. Bayan an nika, sai a tankade a jika a ruwa yadda zai yi daidai da alala.
3. A jajjaga attaruhu a zuba, a yanka albasa a zuba, a zuba mai dai dai misali da kayan dandano.
4. A dafa kwai a bare a yayyanka
5. Sai ana zubawa a Leda ko gwangwani ana cilla kwan da aka yanka. Sai a turara.
Ana ci da miyar jajjagen albasa ko kuma yaji da manja.
A ci dadi lafiya.
© Alummata

Leave A Reply

Your email address will not be published.