Filin Girke Girke Yadda Ake Yin Miyar Edikan IKong.

Yadda Ake Yin Miyar Edikan Ikong

Miyar Edikan Ikong ba miyar Hausawa ba ce, sai dai miya ce da al’ummar Bahaushe ya kamata ta mika hannu ta karba, ta runguma saboda armashin miyar a baki da kuma dimbin alfanunta ga lafiya.

Miyar Edikang Ikong miyar kabilar Efik ce. Ita kuwa kabilar Efik tushensu na jihohin Cross River da Akwa Ibom a kudancin Nijeriya.

Su ne kabilar da ake kira da Calabar saboda wani adadi mai yawa na Efik sun fito ne daga garin Calabar, babban birnin jihar Cross River. Ga dai yadda ake shirya miyar ta Edikang Ikong:

Kayan Hadi:

Alayyahu
Ganyen Ugu
Ganyen Gurai (water leaves)
Manja
Naman sa
Ganda
Kayan ciki
Cray fish
Hanta
Busasshen kifi
Albasa
Attaruhu
Gishiri
Sinadarin Dandano
Curry
Thyme
Citta
Fafarnuwa…… da sauran kayan kamshi.

Yadda Ake Girka Miyar Edikang Ikong
Da farko dai za ki sami tukunya, ki zuba, namanki, da gandarki, da kayan ciki (bayan kin wanke su da kyau). Ki sa musu albasa isasshe, da thyme, curry, da sinadarin dandano da gishiri, citta, da tafarnuwa. Ki zuba wadataccen ruwan da zai dafa su, ki aza bisa wuta ki barsu su dahu sosai.

Bayan kin tabbatar da dahuwarsu sai ki sami busasshen kifinki, ki wanke shi tsaf. Wurin wankewar ki dan saka gishiri, bayan kin yi wankewar farko, sai ki saka masa ruwan zafi sannan ki tsane shi, sai ki sa a cikin naman ki da ya dahu, ki bar shi ya yi kamar minting 8.

Bayan ruwan tafasan namanki ya yi kasa sosai, don miyar ba a cika wa miyar Edikang Ikong ruwa, sai ki zuba jajjagaggen taruhu, cray fish, da kuma manja, sa’annan ki jujjuya, sai ki barshi ya dahu na kamar minti 5, sa’annan ki saka sinadarin dandano.

Sai ki dauko ganyen alayyahunki da na water leaves da tuni dama kin yanka kin wanke kin kuma tsane, ki zuba akan hadin miyar.

Sai ki tona miyar ta yadda ganyen da kayan hadin za su hautsina sosai, sai ki barshi na ‘yan mintina.

Bayan ‘yan mintina sai ki zuba ganyen Ugunki, ki jujjuya, zaki ga miyan duka ya kame babu ruwan miya a cikin sa sai dan kadan, sai ki dan bashi mintina ki rage wutan yadda ganyen za su turaru.

Za a iya ci da Sakwara, tuwo, teba, farar shinkafa da dai sauransu

A lura: Za ki iya dafa gandarki daban tunda shi yana da tauri, wasu kuma suna tafasa dukkan naman da zasu yi amfani dashi.

Miyar bata bukatar kayan miya kamar yadda muke yin miyarmu, tarugu 3 zuwa 5 ya isa.

Sannan miya ce da ke da bukatar nama isasshe. Miya ce mai mutukar kara lafiya saboda ganyayykin da aka yi amfani da su.

Ina fatan za ku gwada.

® Alummata.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.