Gaskia tayi halinta – Zancen Aisha Buhari ya tabbata

Kama lawan Daura baizo da mamaki ba ganin irin yawan mutane da sukayita kiran gomnati ta dau mataki akansa. 

Lawan Daura yana daga cikin yardadun mutane a gomnatin Buhari saidai a kwanannan aka sallameshi daga aiki sakamakon rufe kofar majalisa da ya bada umarnin ayi.

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari tun dadewa ta furta wasu kalamai akan tshohon shugaban hukumar DSS Lawan Daura wanda Mukaddashin shugaban kasa ya kora ranar a wannan watan auguat da muke ciki.

A baya Aisha ta bayyana irin yadda wasu mutane suke yiwa gomnatin buhari zagon kasa amma hukumomin kasar basu amince da zancen nata ba hasali ma mijinta nata Buhari ya fito yace ba aikinta bane fadin kura kuran gomnatin aikinta kawai girka abinci ne a kitchen.

Saidai a kwanannan korar Lawan Daura tasa gomnatin ta gane cewa ashe kalan nata  gaskia ne.

Ana tuhumar lawan daura da wawurar makudan kudade bilyan 70  kuma angano bilyan 21 da bindigogi 4000 da kuma katin zabe 700 a gidansa. Wannan ya nuna irin yadda ya dade yana yaudarar shugaba Buhari bayan irin yadda daya samu daga gareshi.

Akwai mutane dadama dake yaudarar wannan gomnati amma ta nuna amincewa dasu saidai alummar nigeria sun saka ido domin ganin yadda zara kaya idan aka bankado asirinsu.

Source: https://ift.tt/2nwrFuK

Leave A Reply

Your email address will not be published.