Gawa Ta Kama Me Wanke Ta A Jahar Plateau Jos !

 yadda Ake sallar gawa

Gawa Ta Kama Mai Wanka A Jahar Plateau Jos!

Daga Shafin Arewa 24

Wannan abin al’ajabi ya faru ne a lokacin da ɗan uwan mamacin yake shiryashi a ɗakin a jiye gawarwakin, lokaci kaɗan kafin fara bikin binne shi.

Iyalin mamacin waɗanda suka kasance a wurin haɗa gawar sun ranta a nakare, lokacin da suka ga gawar Choji Zeng ta riƙe hannun ƙaninsa mai suna Gyang Zeng.

Hargitsin dai ya janyo hankalin mai kula da ɗakin ajiye gawar wanda ya zo ya taimaka wajen ɓanɓare hannun Gyang da Choji ya riƙe.

Ƴan uwan dai suna zaune tare a unguwar Juma’a dake yankin Abatuwa a birnin Jos, Choji mai shekaru 35 ya rasu ne bayan gajeriyar jinya.

Ɗan uwan mamacin Gyan Zeng ya tabbatarwa da Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa NAN, faruwar lamarin.

©Zuma Times Hausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.