Gidauniyar Jaruma Nafisa Abdullahi Ta Samu Tagomashi

Nafisa Abdullahi
Gidauniyar Jaruma Nafisa Abdullahi ta gudanar da gagarumin taro a karon farko a jihar Kaduna, Gidauniyar mai suna (Love Lough Foundation) Jarumar ta kirkire ta ne, domin taimakon Al’umma da kuma tsamosu daga kangin Talauci da Fatara.

Taron wanda aka gudanar dashi a ranar Asabat 26nv wannan watan da muke ciki, Taron ya samu tagomashi kwarai da gaske, ta yadda ya samu halartar manya manyan mutane daga sassa daban daban na Nigeria.

Cikinsu harda shugaban Majalisar Wakilan Jahar Kaduna Alh. Aminu Abdullahi Shagali, Inda ya gabatar da kyautar tsabar kudi Naira milliyan daya da rabi ga wannan gidauniya karkashin  wakilcin Majalisar dokokin jahar Kaduna.

Ali Artwork

Hakanan shima a nashi bangaran, Fitaccen shahararran dan wasan barkon cinnan da ake yiwa lakabi da Ali Artwork, Kuma shugaban sabuwar kungiyar nan ta Kwankwasiyya Nigeria, ya bada kyautar zunzurutun kudi har Naira Dubu Dari Da Hansin ga wannan Gidauniya .

Leave A Reply

Your email address will not be published.