Girke Girke : Amfanin Shan Miyar Kuka Ga Lafiya Da Yadda Ake Sarrafa Ta

Girke Girke : Amfanin Shan Miyar Kuka Ga Lafiya Da Yadda Ake Sarrafa Ta

Girke Girke : Amfanin Shan Miyar Kuka Ga Lafiya Da Yadda Ake Sarrafa Ta

Ganyen kuka wanda da ita ake miyar kuka nada matukar amfani ga lafiyar dan Adam, tana dauke da sinadarai da dama wanda suka hada da ‘Vitamin C’, ‘Vitamin A’, ‘Beta Carotene’, ‘Potassium’, ‘Calcium’ da saura da dama.
Wadannan Sinadarai kuma na taimakawa wajen magance wasu matsaloli da cututuka kamar su tari, tsutar ciki, ciwon koda, ciwon asthma, majinar dake taruwa a kirji da sauransu.
Yara da dama basu cika son miyar nan ba sakamakon Kasancewar yadda wadansu mata ke girkawa, Miyar dai nada gwanin dadi idan aka sarrafata da kyau
Abubuwan da za a bukata wajen sarrafa miyar sune:
• Kuka
• Banddar kifi
• Kaza/nama
• Citta
• Attarugu
• Albasa
• Magi
• Man shanu
• Daddawa
Man shanu

Hadi


Da farko Uwar gida za ta wanke Kazarki ko nama yadda ya kamata sannan ta daura a wuta. Ta yayyanka albasa da tafarnuwa da dan gishiri kadan sosai, har hadin ya tafasa. Sannan ta dauko kifi banda kamar daya ta wanke da ruwan zafi sannan ta zuba. Ta jajjaga attarugu hade da daddawa sai sunyi laushi sannan ta zuba. Ta samu garin citta kadan ta zuba da magi.

Idan an fara jin kamshin kifi ya bayyana, alama ce cewa kifin ya nuna sannan a tsame kazar ko namar a ajiye a gefe sannan a debo garin kuka a rika kadawa kadan-kadan ta yadda ba za ta yi gudaji ba. Sannan ta rage wuta ya dan sake tafasa kadan. Idan tana bukatar sanya tokar miya, sai ta zuba kadan ta sake gaurayawa sannan ta sauke.

A tuka tuwon dawa ko na masara ko kuma na shinkafa sannan aci da man shanu.
Mun Kofo Ne Daga Shafin © Alummata

Leave A Reply

Your email address will not be published.