Gomnan sokoto Aminu Tambuwal ya fice daga APC

Gomnan jihar sokoto Aminu Waziri Tambuwa ya sanarda ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki a yau laraba.

Tambuwal ya yanke shawarar fita daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP ne sakamakon takun saka dake tsakaninsa da shugabancin jamiyyar.

Tun watan daya gabata ne aka fara jiyo gomnan da wasu takwarorinsa suna ambato shirin nasu na fita daga APC matukar ba’a samu daidaito tsakani ba.

Ana cigaba da barin jamiiyyar ta APC amma dai har yanzu abinda shugabannin jam’iyyar a matamin kasa suke fadi shine ko ajikinsu. Saidai masu sharhi kan al’amuran siyasa suna ganin hakan zai iya tasiri ga komawar jam’iyyar APC mulki a zaben 2019.

Source: https://ift.tt/2O2wd75

Leave A Reply

Your email address will not be published.