Happy Juma’a : Akwai Wata Sa’a A Ranar Juma’a Karanta Kuji !

AKWAI WATA SA’A A RANAR JUMA’AH:

An karbo Hadithi daga Abu Hurairah (R.A), Hakika Manzon Allah (S.A.W) Ya ambaci ranar Jumu’ah, Sai Ya ce: “A cikinta akwai wata Sa’a, wadda idan bawa yayi daidai da ita yana tsaye yana Sallah ko yana rokon Allah, Allah zai ba shi dukkan abinda ya roka”. (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Wannan Hadithi yana koyar damu dagewa da yawaita Ibada a dukkan yinin Jumu’ah. Duk da Malamai sunyi sabani a kan wannan lokaci. Shawara a nan Ita ce muyi kokarin game dukkan yinin da ayyukan da’a ga Allah da kuma nisantar hane-hanenSa.

ALLAH YA BAMU IKON DAGEWA DA IBADA KUMA YA SA MU DACE. AMIN.

® www.HausaMedia.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.