Hukumar EFCC Ta Kama Wani Mawallafi A Shafin Internet

A ranar Litinin Dinda ta gabatar ne dai hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa Tareda Masu Yiwa tattalin Arzikin kasa zagon kasa ta Kama Wani Matashi Mai Suna Abubakar Sadik usman Bisa wallafa Wani labari a kafar internet.

Inda Hukumar ta zargeshi da Laifin Aika sakonnin barazana ta internet, Abinda hukumar tace ya sabama Dokar.

Sai dai Wasu rahotanni na cewa an Kama shine sabo da wani labari daya wallafa a kan shugaban hukumar ta EFCC, Ibrahim Magu, wanda labarin bai yiwa hukumar dadi ba.

Sai dai tuni kungiyoyin kare hakkin bil adama da masu fafutuka A shafin Internet Suka soki hukumar ta EFCC kan wannan mataki data dauka.

Inda a Wani Bangaren kuma Kungiyar SERAP dake yaki da cin hanci da rashawa da kuma kare hakkin dan adam ta zargi hukumar ta EFCC da wuce gona da iri kan kamun.

Sai dai daga baya hukumar ta EFCC ta bayar da belin mawallafin tareda sharudda da kuma kawo Mutanen da zasu tsaya masa domin bada belin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.