INEC ta bada sanarwar ranarda za’a rufe rijistar katin zabe

Hukumar zaben Nigeria INEC ta sanarda cigaba da yin rijistar katin zabe har zuwa ranar 27 watan August da zata ruder rijistar  a duk fadin nigeria.
Solomon Soyebi Kwomishinan zabe kuma shugaban kwamiti dake wayarda kan mutane a fannin zabe yace sun yanke hukuncin ne bayan wata tattaunawa da suka gudanar a abuja.
Soyebi yace za’a rufe rijistar amma wadanda sukayi zasu cigaba da karbar katin zabensu har zuwa sati 1 kafin gudanarda zaben a Nigeria.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Nigeria da basuda katin su daure suje suyi rijiata kafin a rufe wadanda sukayi kuma suje su karba da zarar katin ya fito.
Hukumar INEC itace hukumar dakeda alhakin duk wani abu daya shafi zabe a Nigeria.

Source: https://ift.tt/2LMQKAh

Leave A Reply

Your email address will not be published.