Jadawalin Sunayen Manyan Masu Kudin Nigeria Da Abubuwan Dasu Mallaka (2017)

Jadawalin Sunayen Manyan Masu Kudin Nigeria Da Abubuwan Dasu Mallaka

Shafin “Forbes” Wadanda Sukayi Fice Wajen Bayyana Hamshakan Masu Kudi Na Duniya, Sun Fitar Da Jadawalin Sunaye Goma Na Wadanda Sukafi Kudi a Nigeria.

1* Aliko Dangote: Shine mutumin da ya fi kowa kudi a Nijeriya da kuma nahiyar Afirka baki daya, Dangote shine bakin mutum mafi karfin tattalin arziki a duniya. A shekarar 2014, Dangote ya shiga sahun masu kudi na duniya inda ya zamto mutum na 24 da yafi kowa kudi a duniya amma saboda matsin tattalin arziki da ake ciki yanzu wanda ya kawo faduwar darajar Naira, Dangote ya koma sahun kasa da 100.

2* Mike Adenuga: Shine mutum na biyu da yafi kowa karfin tattalin arziki a Nigeria, Mike Adenuga dankasuwa wanda yake harkar manfetur, Gas da kuma Sadarwa. Ya mallaki kamfanin sadarwar Glo da kuma kamfanin mayi na Conoil sannan yana da zunzurutun kudi har dalar Amurka Biliyon $10.5.

3* Femi Otedola: Mai kamfanin mayi na Zenon Oil and Gas da kuma Forte Oil Plc. Sannan yana wasu harkarkoki da suka hada da cinikayyar gidaje. Ya kasance a sahu na biyu domin shi ma ya mallaki dalar Amurka $2.3.

4* Folorunsho Alakija: Hamshakiyar yar kasuwa macen da tafi kowacce mai dankwali dukiya a Afirka ta kasance ta hudu a jerin masu kudi a Nigeria domin ta mallaki kudin da ya kai dalar Amurka biliyon $2.1.

5* Theophilus Danjuma: Tsohon Babban Hafsan sojan kasarnan daga shekarar 1975 zuwa1979. Wanda yanzu haka shine mai kamfanin Athlantic petroleum, yana matsayi na biyar a jerin masu kudin Nigeria sakamakon mallakar dalar Amurka biliyon $1.7 .

6. Abdussamad Isiyaka Rabiu: mai kamfanin BUA Group wadanda suke sarrafa suminti da suga da kuma wasu harkokin kasuwanci yazo matsayi na shida da mallakin dalar Amurka biliyon $1.5.

7. Tony Elumelu: yazo matsayi na bakwai inda ya mallaki dalar Amurka biliyon $1.4 .

8* Orji Uzor Kalu: Tsohon gwamnan jihar Abia. Hamshakin dan kasuwa mai harkokin da suka hada da harkar mayi da sauransu ya shiga harkar kasuwanci tun yana shekara 19 bayan da aka kore shi a jamia sakamakon samun shi da hannu wajen tada tashin tashina a tsakanin dalibai. Yanzu haka ya mallaki dalar Amurka biliyon $1.1 .

9*. Jim Oviah: Wanda shi ya assasa bankin Zenith kuma shi yafi kowa hannun jari mafi yawa a banki, ya zamanto na tara a jadawalin hamshakan masu kudi sakamakon mallakar dalar Amurka biliyon $1 billion.

10*. Oba Otudeko: Shugaban kuma mai kamfanin honeywell sannan shugaban FBN Holding ya zo a matsayi na goma da dalar Amurka miliyon $650.

Leave A Reply

Your email address will not be published.