Jamian Yan Sandan Jihar Akwa Ibom Sun Kama Wani Mutumi Bisa Zargin Kisan ‘Yarsa

Jamian Yan Sandan Jihar Akwa Ibom Su Kama Wani Mutumi Bisa Zargin Kisan ‘Yarsa.

Yan sandan sun cafke Wannan mutumnne mai suna Eno Akpan bayan ya kashe yarsa yar shekara 1 da haihuwa mai suna Favour.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Eno Akpan dan asalin kauyen Ikot Akpan Udo dake cikin karamar hukumar Ikot Abasi na jihar Akwa Ibom mai shekaru 30 wanda ke kula dad akin bautan gargajiya dake kauyen ya kashe yarsa ne da adda.

Rahotanni sun nuna cewa Eno ya samu matsala tsakaninsa da matarsa, wanda ya kai ga yayi mata duka, bayan sun gama fadan ne sai matar ta gudu ta koma gidan mamanta, inda ta bar karamar yarta Favour a gidan mijin nata.

Jami’a mai magana da yawun hukumar yansanda ta jihar Akwa Ibom Cordelia Nwawe tace Eno ya kira matarsa tazo ta dauki yarinyar, amma da taki zuwa, sai kawai ya samo adda ya sare Favour a kai da baya. Yarinyar ta rasa ranta sanadiyyar raunukan da ta samu daga saran.

Jami’ar yansanda tace “a ranar 23 ga watan yulio da misalign karfe 7:30 na dare, Blessing ta kawo mana kara cewa sun samu matsala da mijinta Eno Akpan. A dalilin haka mijin ya mata duka. “daga nan sai ta gudu daga gidan, ta koma gidan su, ta bar yarta a gidan mijin nata. Mijin ya bukace ta da ta dawo ta dauki yarinyar, amma matar taki. Daga nan ne fa mijin ya dauki adda ya Sassari yarinyar a bayanta da kanta. Nan take ta mutu.” Nwawe tace ana cigaba da bincike kan lamarin.

Sai dai shi Eno yace ransa y abaci ne bayan matarsa tayi lattin dawowa daga kasuwa inda take siyar da kifi. Ya tabbatar da cewa ya sa ma matarsa hannu, amma yace ya so ya sari matar da adda ne, amma sai ta gudu sai addan ya sare yarsu.

“ta tafi kasuwa don siyar da kifi ne, amma da ta dawo, sai na tambayeta dalilin da yasa ta yawan dawowa latti daga kasuwar. “amsar da ta bani yayi matukar bata min rai, ni kuma sai nah au dukanta. Ina daukan adda na don in sare ta, sai ta wurga yarinyar mu daida inda addan ya sara, sai ya sauka akan bayanta da kanta.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.