Jaririya ‘Yar Wata Shida da Akai Wa Fyade Ta Kamu Da Cuta

Jaririya ‘Yar Wata Shida da Akai Wa Fyade Ta Kamu Da Cuta

Daga Balarabe Yusif Gajida

Yarinyar’ yar kimanin wata shida Khadija Bashir, ta gamu da wannan iftila’i ne yayin da ake zargin mijin kawarta ya yi mata fyade, a Unguwar Fage da ke cikin birnin Kano, kawowa yanzu dai wannan magana na gaban kotu amma an tabbatar wannan yarinya ta kamu da wata irin cuta.

Wata likita a Asibiti da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da cewar yarinyar ta kamu da cutar da ta bata mata jikinta gabadaya.

Wakilinmu da ya je Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, ya gane wa idonsa yadda halin da yarinyar ta ke cikin yanayin na ban tausayi, sannan kuma akwai wani rami a karkashinta wanda girmansa ba zai buya ba da kuma wasu raunika a ko ina a jikinta.

Abu mafi muni shine da Zuma Times ta lura da shi shine yarinyar ‘yar wata shida da ta gamu da iftila’in fyade kafahunta sun fara kankancewa wanda zai iya tsorata duk wanda ya gani.

Mahaifin yarinyar, MalamBashir Adam ya ce sun lura kafafun yarinyar biyu sun sami matsala domin kullum kara kankacewa.

Mahaifin ya bayyana cewa mutumin da ya yi wa ‘yarsa wannan ya ma girme shi inda ya ce hakan ya faru ne a  lokacin da matarsa ta ziyarci yar uwata a unguwar Fage da ke Kano.

“Abinda ya faru shine kawar matarsa ta dauki yarinyar zuwa gidan mijinta da ke kusa da gidan da suke, sannan daga bisani ta dawo da yarinyar a cikin wani yanayin da a wannan lokacin  babu wanda zai iya gane mai ya faru da ita ba.”

Ya ce, an kira shi ne a waya a kace ya dawo gidan ‘yar uwarsa da ke Fage domin akwai wata matsala da ta faru da ‘yarsa, inda ya ce, isarsa sai ya lura jini da maniyi suna fitowa daga gaban yarinyar.

Baban yarinyar ya kara da cewa an yi fyade ne tun cikin watan Faburairu, kuma tun wannan lokacin yarinyar na samun kulawar likitoci shi kuma wanda ake zargi ‘yan sanda sun kamashi kuma sun gurfanar da shi gaban kotu.

A kalamansa ya ce, “watanni uku da suka wuce yarinyar na cikin matsala, an mata aiki saboda yanayin lafiyarta,  sakamakon zubar da jini da fitsari da kuma ruwa duk a lokaci daya ta gabanta.

“Khadija ba ta iya barci sai kuka, mahaifiyarta da ni ba mu barci, kuma ni ke dawaini da kudin maganinta da kuma dan taimakan da muke samu daga wajen mutane kuma muna sayen maganin da zan iya ne kawai ba wanda ya dace ba.”

Ya bayyana cewa ya sami matsin lamba sosai daga Hukumar Asibitin akan kada ya yarda ya bari a yada abin a kafafen yada labarai amma ya kasa daurewa, inda ya koka akan rashin inganci wasu labarai da kafafen yada labarai inda ya ce, matar wanda ya yi wa ‘yarda fyade  ta bayyana mutuwar ‘yar tasa a radiyo a daidai lokacin da ya ke asibiti tare da yarinyar.”

Mahaifin yarinyar ya koka  akan yawan kirasa da ake a waya kullum domin yai watsi da kara da aka kai wanda ake tuhuma.

Ya ce, ya sami saukin kuran ne lokacin da wasu suka yara suka kwance masa waya a yayin da ya bar harabar asibitin.

Duk wadanda ake zargin Mata da Mijin suna gidan yari har zuwa ranar da za a kara komawa kotu.

Sai dai kuma a yayin rubuta wannan rahoton, Zuma Times ta samu labarin cewa likitoci sun sallame su daga asibitin duk da korafin da mahaifan ke yi cewa har yanzun ‘yarsu ba ta ji sauki ba.

©Zuma Times Hausa

Leave A Reply

Your email address will not be published.