Jaruman fim din Nollywood 6 da suka musulunta

Sanannen abu ne ga jaruman fina finan Nollywood musamman mata suna yawan sauya addini su bar wanda suka taso aciki su koma wani. Mafi yawanci sunfi komawa musulunci wani lokacin har hadawa suke shiryawa don tafiya kasar Saudia domin gudanarda aikin hajji. 
Moji Olaiya 
Haifafiya ce ga tsahon mawaki Victor Olaiya wanda krista ne. Amma mahaifiyarta kuma musulma ce kafin daga bisani ta koma krista. Moji tace “Musulumci addini ne na zaman lafiya wanda baya bukatar wani fasto da zaka nemi yardarshi kafin Allah yayarda dakai. Addini ne da zaka iya addua kai kadai kuma Allah ya amsa kamar yadda nasha yin addua kuma in samu biyan bukata. 
                                                               Vivian Metchie  
Diya ce ga iyaye masu bin darikar CHATOLIC mahaifiyarta kuma tana bin darikar DEEPER LIFE. Tayi aure harda ‘ya’ya hudu daga bisani suka rabu da mijinta kuma tanada ‘ya’ya hudu sannan daga baya ta bar addinin Krista zuwa Islam a wata hira da akayi da ita ta bayyana littafin Qur’an matsayin littafi da yafi kowanne samarda nutsuwa a zuciya hakazalika kuma ta sauya sunanta zuwa FAREEDA. 
                                                               Liz Da Silva
Liz Da Silva ‘yar addinin kristan ce wacce aka taba zargi da haihuwa da wani shugaban kungiyar NURTW amma daga baya ta auri wani musulmi har sun haifi diya mace bayan haihuwarsu saita musulunta ta sauya suna zuwa Aisha. 
                                                                  Lizzy Ajorin
Lizzy Ajorin mahaifinta krista ne mahaifiyarta kuma musulma ta girma ne da addinin mahaifinta saidai a shekarar 2013 kuma tayi sha’awar sauya addinin ta koma musulma. Lizzy tace ta sauya sunanta zuwa Aisha kuma tanada diya mace sunanta rufaidat. Ta bayyana irin farinciki da nustuwa data samu a addinin musulunci.
                                                                 Laide Bakare
Laide Bakare an haifeta ne acikin addinin Krista kuma sun rabu da mijinta musulmi bayan wata rashin fahimta da suka samu. 
Laide ta sake sabon aure da wani Shahraren mai kudi a jihar lagos mai suna Alh Tunde Orilowo wanda akafi sani da ATM sanadiyyar Aurensa ta musulunta ta shiga jerin matansa. 
Lola Alao
Lola Alao itace wacce ba’a jima da musuluntarta ba. Ta musulunta ne a hannun wani babban malamin musulunci hakan yasa jamaa da dama sun watsa labarinta a shafin Facebook. Ta bayyana kanta itama a shafin Instagram inda tayi wata gaisuwa ta addinin musulunci. Tayi sabon aure a 2013 da wani mazaunin kasashen turai bayan ta rabu da mijinta na farko sakamakon wasu zarge zarge. 

Source: https://ift.tt/2AJ9dsh

Leave A Reply

Your email address will not be published.