Jihar Benue ta samu sabon kwamishinan ƴansanda

Sabon kwamishinan ƴansanda, Besan Dapiya Gwana, ya fara aiki a rundunar ƴansandan jihar Benue.

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, DSP.Moses Joel Yamu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Makurdi.

Yamu ya ce kafin ya kama aiki a matsayin kwamishina a jihar Benue, Gwana ya kasance kwamishina dake kula da bangaren bincike a hedkwatar rundunar ƴansanda ta kasa.

Gwana zai maye gurbin,Fatai Owoseni wanda aka dauke shi daga jihar a makon da ya wuce.

Jihar Benue ta dade tana fama da rikici da ya jawo asara rayukan mutane da dama tare da raba wasu dubbai da gidajensu.

Source: https://ift.tt/2AlZmIw

Leave A Reply

Your email address will not be published.